NAU'O'IN AZABAN QABARI {01}
thanks!!!
NAU'O'IN AZABAR QABARI {1}
*******************************
Da sunan Allah Mabuwayin Sarki Gagara-Misali. Wanda ya
halicci 'Yan Adam daga Qasa, Kuma ya sanyata ta zama
Makwancinsu bayan rasuwarsu, sannan kuma daga
cikinta zai tashesu aranar babban taro.
Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da Allah ya
zabeshi ya fifita Halittar jikinsa da halayensa da nasabarsa
fiye da na sauran halittunsa baki daya, tare da iyalan
gidansa da Sahabbansa Taurarin Shiriya.
Bayan haka, kamar yadda daliban Zauren Fiqhu suka sani,
mun sha kawowa ayoyi, hadisai da hikayoyi wadanda
suke tabbatar da cewa azabar Qabari gaskiya ce. Harma
mun kawo zancen da Qabari ke yi yayin da za'a sanya
Ma'abocinsa cikinsa.
Yau kuma in sha Allah zamuyi magana ce akan kala-kalar
azabobin Qabari da kuma yadda suke gudana.
Kamar yadda muka sha gaya muku acikin darussan
Zauren Fiqhu da suka gabata, ita dai azabar Qabari tana
gudana ne akan jiki da ruhin Bil Adam. Ga nau'o'inta nan
kamar haka :
1. DUKA DA GUDUMAR BAQIN QARFE : Akwai ruwayoyi
daban-daban ta hanyoyi masu yawa akan wannan. Misali
kamar hadisin da Ibnul Jawzee ya ruwaito ta hanyar
Sayyiduna Abu Umamatal Bahiliy (ra) yana cewa :
"Manzon Allah (saww) yaje maqabartar baqee'a sai ya
tsaya akan wasu Qaburbura guda biyu. Sai yace "SHIN
ANAN WAJEN KUKA BINNE WANE DA WANE?.
Sai Sahabbai sukak ce "Kwarai kuwa". Sai yace : "To yanzu
gashi nan an zaunar da wane, ana Jibgarsa".
Yaci gaba da cewa : "INA RANTSUWA DA WANDA
NUMFASHINA KE HANNUNSA, YANZU HAKA ANYI MASA
WANI DUKA GUDA 'DAYA WANDA BABU SAURAN WATA
JIJIYA AJIKINSA FACHE SAI DA TA TSINTSINKE.
"KUMA GASHI NAN QABARINSA YANA TASHI DA WUTA.
KUMA GASHI NAN WALLAHI YAYI WANI EEHU WANDA
DUKKAN HALITTU SUNA JINSA IN BANDA MASU NAUYIN
NAN GUDA BIYU, WATO MUTANE DA ALJANU".
"BA DON KOKWANTON DAKE ZUKATANKU BA, DA KUMA
QARI ACIKIN ZANCE, DA WALLAHI SAI KUNJI IRIN
ABINDA NAKE JI.
"AMMA WANE, LAIFINSA SHINE YA KASANCE BA YA YIN
TSARKI DAGA BAWALI. AMMA WANE KO WANCE, YA
KASANCE YANA CIN NAMAN MUTANE NE".
lIbnu Jareer ya ruwaito hadisi acikin littafin tafeerinsa ta
hanyar Asbaat daga Suddiy, yana cewa "Sayyiduna Al-
Bara'u bn Aazib (ra) yace "Hakika shi kafiri bayan an
sanyashi acikin Qabarinsa, sai wata dabba tazo masa
wacce idanuwanta biyu tamkar Kaskon wutar dalma
suke.
"Tare da ita akwai wata Qatuwar guduma ta baqin Qarfe
wacce idan ya jibgeshi da ita atsakanin kafadunsa, sai
zabga eehu. Babu wani wanda zai jiyo Eehunsa fache sai
ya tsine masa. Kuma babu wata halittar da ba zata jiyoshi
ba, sai dai nauyayan nan guda biyu (wato) Aljanu da
mutane".
Hakanan akwai wata ruwayar shigen irin wannan daga
Dhahhak (ra).Imam Lalkaa'iy ya ruwaito da isnadinsa ta hanyar
Muhammad ibnul Munkadir yace "Labari ya iskeni cewa
Allah yana salla'da ma kafiri acikin Qabarinsa wata dabba
wacce take Makauniya a hannunta akwai bulala ta Qarfe.
Kayinta kamar girman rakumi. Zatayi ta jibgarsa har zuwa
tashin Alqiyamah. Ba ta ganinsa, ba ta jin sautinsa
ballantana ta tausaya masa".
2. MACIZAI DA KUNAMU : Nau'in bala'i na biyu wanda ake
salla'da ma masu laifi acikin Qabarinsu shine Macizai da
kunamu.
Isnadin Hadisi daga kan Ibnu Wahbin har zuwa kan
Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Manzon Allah (saww)
ya tambayi Sahabbai (ra) "Shin ko kun san akan menene
aka saukar da ayar nan " ﻓﺈﻥ ﻟﻪ ﻣﻌﻴﺸﺔ ﺿﻨﻜﺎ؟". (Lallai akwai
rayuwa mai Qunci agareshi).
Shin ko kun san mecece rayuwa mai Qunchi?" sai suka ce
"Allah da Manzonsa ne ya sani".
Sai Manzon Allah (saww) yace (Tana nufin) Azabar da
za'ayi ma kafiri acikin Qabarinsa ne.
"INA RANTSUWA DA WANDA RAI NA YAKE HANNUNSA,
HAKIKA ZA'A SALLA'DA MASA TINNEEN GUDA CHASA'IN
DA TARA NE".
"SHIN KO KUN SAN MENENE TINNEENI?"
"MACIZAI NE GUDA CHASA'IN DA TARA. KOWACCE
MACIJIYA TANA DA KAYUWA GUDA BAKWAI (ACIKIN
WATA RUWAYAR KUMA AKA CE KAYUWA GUDA TARA).
"ZASU RIKA HURA (GUBA) ACIKIN JIKINSA, KUMA SUNA
CIZONSA SUNA 'DAYE NAMAN JIKINSA HAR ZUWA RANAR
ALKIYAMAH".(Baqiyyu bn Mukhallad ne da Imamul Bazzar suka
ruwaito shi).
Imamu Ahmad da Ibnu Hibban sun ruwaito wani Hadisin
daga Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) yana cewa:
"Za'a sallada ma kafiri Macizai guda chasa'in da tara
acikin Qabarinsa zasuyi ta cizonsa har Alqiyamah ta tashi.
Da ache daya daga cikin wadannan Macizan zai hura
Qasa, da babu wani koren abu da zai sake tsirowa
abayanta".(Imamu Ahmad da Ibnu Hibban suka ruwaito shi).
Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) da Almajiransa suka
tambayeshi akan abinda ake nufi da "MA'EESHATAN
DHANKAN" (Wato rayuwa mai Qunchi), Sai yace "Ita ce
rayuwar kafiri acikin Qabarinsa.
Qabarin nasa zai matseshi har sai Qasusuwan
haqarkarinsa sun shige cikin junansu, har sai yayi burin
gara ma ya fito daga Qabarin ya shiga wuta".
Wani hadisin kuma daga Nana A'isha (ra) tace Manzon
Allah (saww) yace: "Za'a aika ma Kafiri wasu Jibga-jibgan
Macizai guda biyu, 'daya ta wajen kansa, 'daya kuma ta
wajen Qafafunsa Zasuyi ta cizonsa. Duk Sanda suka 'daye
fatar jikinsa sai fatar ta dawo har zuwa tashin
Alqiyamah".
Hakanan Ibnu Abid dunya ya ruwaito wani hadisin ta
hanyar
Masrouq
yana cewa "Babu wani wanda zai mutu
alhali yana zina ko shan giya ko kuma wani abun alfasha
fache sai Allah ya sallada masa Manyan Macizai acikin
Qabarinsa. Suna cizonsa suna cinye naman jikinsa har
tashin Alqiyamah".
Ya Allah ka kiyayemu daga azabar Qabari. Ka gafarta
mana zunubanmu, kayi mana afuwa busa laifukanmu
don albarkar Annabinka(saww).
Anan zamu tsaya sai acikin kashi ba biyu zamu dora daga
nan. In sha Allahu.
DAGA ZAUREN FIQHU (09-01-2017) 07064213990 Kuje
kuyi "liking" din shafinmu na facebook @Zaurenfiqhu